in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban yankin kasar Sin ya yi musaya yadda ya kamata da yankin Taiwan a shekarar 2012
2013-01-16 16:59:13 cri

Yau Laraba 16 ga wata, kakakin ofishin kula da harkokin yankin Taiwan na kasar Sin Yang Yi, ya kira wani taron manema labaru, inda ya bayyana cewa, a bara, babban yankin kasar ya yi musaya yadda ya kamata, a bangarori daban-daban yankin Taiwan, al'amarin da ya karfafa dangantakar dake tsakanin sassan biyu.

Yang Yi ya nuna cewa, akwai muhimman nasarori hudu da aka samu a wannan fanni, wato da farko, yawan mutane ko kungiyoyi da suka shiga wannan hulda ya karu matuka, kuma halin da ake ciki a wannan fanni ya samu kyautatuwa sosai, sannan matakin ya habaka mu'ammala tsakanin fararen hula, tare da samar da karin nasarori a fannin yin mu'ammala.

A ganinsa, mu'ammala da ake yi zata yi tasiri matuka, wajen kara yin musayar ra'ayi tsakanin jama'ar yankunan, da habaka dangon zumunci tsakaninsu.

Ban da haka, Yang Yi ya ce, Sin na nuna matukar rashin jin dadi ga matakin da Amurka ta dauka, na sayarwa yankin Taiwan makamai, kuma yana fatan Amurka za ta mutunta hadaddiyar sanarwa guda uku, da aka cimma tsakanin Sin da Amurka, tare da bin manufar kasar Sin guda daya tak a duniya.

Hakazalika, babban yankin na kokarin karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, da kuma sassauta halin da ake ciki tsakaninsu. Yace an taba ba da wata shawara ta neman bangarorin biyu su aiwatar da musayar ra'ayi ta fuskar aikin soja, da tattauna kan yadda za su kafa wani tsarin amincewa da juna a wannan bangare.

Daga nan sai ya jaddada cewa babban yankin kasar Sin zai ta ci gaba da sa kaimi ga kiyaye zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China