in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kaiwa dalibai a arewa maso gabshin Najeriya
2013-10-01 16:55:33 cri
A ranar Litinin ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah-wadai da mummunan harin da aka kaiwa wasu dalibai a arewa maso gabashin Najeriya,yana mai cewa,babu dalilin kai irin wannan hari.

Wata sanarwa da kakakin Mr Ban Ki-moon ya bayar, ta ce, babban sakataren na MDD, ya yi Allah-wadai da kashe daliban tare da jikkatu wasu da maharan suka yi a kwalejin koyon aikin gona da ke garin Gujba a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa,Mr Ban ya aike da sakon ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa,gwamnati da kuma al'ummar Najeriya game da wannan danyen aiki.

Bugu da kari sanarwar ta ce, babban sakataren MDDr ya kadu matuka game da karuwar munanan hare-hare da ake kaiwa kan dalibai da malamai a arewacin kasar ta Najeriya,inda ya bukaci da a hanzarta kawo karshen irin wadannan ayyukan ta'addaci marasa dalili.

Har ila yau, Mr Ban ya yi kiran da a zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kuliya, kana a kara daukar matakan da suka dace don hana aukuwar irin wadannan hare-hare nan gaba da kuma tabbatar da kare rayukan fararen hula.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China