Shugaba Jonathan ya bayyana takaicinsa don gane da kisan daliban ne, yayin wata tattaunawar da gidan talabijin mallakar kasar ya yada, yana mai gabatar da ta'aziyyarsa ga iyalai da 'yan uwan daliban da suka rasu sakamakon harin na safiyar Lahadi.
Ya ce manufar wadanda suka kitsa wannan ta'asa ba ta wuce yi wa kokarin da gwamnatinsa ke yi, na yaki da ayyukan ta'addanci kafar ungulu ba. Don haka a cewarsa abu ne a fili, maharan da masu goya musu baya, basa fatan ganin hadin kasan kasar da ma ci gaban ta. (Saminu Alhassan Usman)