Jonathan ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bikin cikar kasar shekaru 53 da samun 'yancin kai a ranar Talatar nan. Ya kuma yi amfani da wannan jawabi wajen sake jajantawa iyalai, da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren da 'yan bindiga ke kaddamarwa a sassan kasar daban daban.
Don gane da batu siyasar kasar kuwa, shugaba Jonathan ya ce 'yan siyasa na gari, su ne ke mai da hankali ga ci gaban kasar maimakon batun zaben dake tafe. Ya ce akwai matukar bukatar kauracewa muggan kalamai, da nuna kiyayya irin ta siyasa, wadanda ba za su taba haifarwa kasar da mai ido ba.
Bugu da kari shugaba Jonathan yace wajibi ne dukkanin zababbu dake kujerun mulkin jama'a, su maida hankali ga aiwatar da tsare-tsare, da zasu ciyar da rayuwar al'umma gaba, maimakon bata lokaci wajen cimma bukatun kashin kansu.
Daga nan sai ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar, da su maida hankali ga daukar matakan da za su bunkasa, tare hada kan kasar waje guda, musamman ma a wannan lokaci da kasar ke fuskantar tarin kalubale.(Saminu Alhassan)