Wani mutum da ake kyautata zaton dan kunar-bakin-wake ne ya tayar da bom a wani barikin soja dake birnin Agadez, abun da ya sa wanda ya jefa bom ya mutu nan take, sa'an nan mutane da dama suka jikkata. Ministan tsaro na Jamhuriyar Nijar Mahamadou Karidjo ya ce, sojoji a kalla 17 ne suka rasa rayukansu.
A can birnin Arlit ma, rahotanni na cewa yau da misalin karfe 5 da rabi na safe, wasu bama-bamai sun tashi a kamfanin Somair mai hakar ma'adanin Uranium mallakar kasar Faransa, lamarin da ya raunata mutane 13. A halin yanzu dai ma'aikatan ceto na Jamhuriyar Nijar sun isa gurin domin gudanar da ayyukin ceto
Wadannan boma-bomai sun tashi ne kusan a lokaci guda.
Har wa yau kuma, ministan tsaro na kasar Nijar Mahamadou Karidjo, ya ce ana kyautata zaton mutanen da suka kai hare-haren kunar-bakin-waken suna da alaka da kungiyar Al-Qaeda, kuma watakila sun shigo kasar ce daga kudancin kasar Libya.