in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron koli na musamman na kungiyar AU
2013-10-11 17:29:50 cri

A ranar jumma'an nan 11 ga wata, aka bude taron koli na musamman na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. A lokacin taron na kwanaki 2, wakilai daga mambobin kasashe 54 na kungiyar za su tattauna batun zargin da babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya ta yi ga shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, sannan kuma, za su kada kuri'a game da ko za su janye jiki daga cikin babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya.

Kafofin yada labaru sun bayyana cewa, dalilin da ya sa aka yi wannan taro, shine sabo da babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya ta bukaci shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da ya je birnin Hague don yin masa hukunci a watan Nuwanba na bana bisa zargin da aka yi masa. A cikin shugabannin kasar Kenya, ban da Kenyatta da aka zarge shi da laifin keta hakkin dan Adam, da kulla makirci da shiga cikin tashe-tashen hankalin da aka samu bayan babban zaben kasar a shekarar 2007, ana kuma zargin mataimakin shugaban kasar William Ruto da aikata wannan laifi. Da ma, babbar kotun tana zargin wadannan mutane biyu, amma bayan da suka zama shugaban kasar Kenya da mataimakin shugaban kasar a watan Maris na bana, wannan zargi ya kara jawo hankalin jama'a. A nasu bangare kuma, shugaba Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto sun musunta zargin da kakkausar suka,sai dai kuma, sun bayyana cewa, za su yi iyakacin kokari don taimakawa binciken da babbar kotun take yi masu.

Kwanan baya, ministar kula da harkokin wajen kasar Kenya Amina Mohamed ta yi jawabi cewa, yanzu, halin da ake ciki ya canja, Kenyatta ya zama shugaban kasar. Kuma a matsayin shugaban kasar, ba zai yiwu ba, ya je babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya bisa tuhumar da ake yi masa, domin abu ne da ba a taba ganin irinsa ba cikin tarihi. Wannan ya nuna cewa, ra'ayin shugaban Kenyatta ya canja.

A wata sabuwa kuma, kasar Kenya tana lallashin kasashen Afrika da kungiyar AU, don fatan ganin daukacin kasashen Afrika zasu matsa lamba ga babbar kotun binciken manyan laifuffuka, don sa kaimi gare ta da ta daina ko kawo jinkiri game da tuhumar Mr.Kenyatta. Game da zargin da aka yi wa Kenyatta, kungiyar AU ba ta amince da wannan ba. Sabo da haka, kungiyar AU ta shirya wani taron koli na musamman cikin gaggawa kafin ranar da za a yi tuhumar a watan Nuwanba na bana. Amma manazarta sun bayyana cewa, shirya wannan taron koli na musamman ya nuna cewa, kasashen Afrika da dama suna bukatar babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya da ta canja halin da take ciki.

A ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2002, aka daddale "yarjejeniyar babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya ta Rome", kuma aka kafa babbar kotun bisa yarjejeniyar, yanzu akwai kasashe 126 da suka daddale wannan yarjejeniya, cikinsu har da kasashen Afrika 34. Ko da yake, akasarin kasashen Afrika sun daddale yarjejeniyar, amma ba su jin dadin yadda babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya take hukuncinta, wadda take shari'a guda 8, da dukkansu suka shafi kasashen Afrika, cikinsu har da kasashen Kenya, Sudan, Libya, Mali, Uganda da sauransu.

Musamman ma bayan da shugaba Kenyatta ya zama shugaban kasar, babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya ta ci gaba da tuhumar sa, abin da ya kawo rashin jin dadi ga wasu kasashen Afrika, kuma sun bayyana cewa, ya kamata kasashen Afrika su rika warware batutuwa da kansu. Har ma wasu shugabannin kasashen Afrika sun bayyana karara cewa, babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya da kasashen yammacin duniya suka yi yunkurin kafa ta, ta zama wata kafa da wasu kasashen suka yi amfani da ita don kawar da shingaye.

Game da wannan, manazarta sun bayyana cewa, kasashen Afrika sun kira wani taron koli na musamman don sake yin la'akari da alakar da ke tsakaninsu da babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya, kuma abin da ya fitar da anniyar jama'a ta nahiyar.

Ko da yake, kwanan baya, shugabannin kasashen Afrika da dama, sun kushe babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya, amma, ban da kasashen Zimbabwe da Habasha, sauran kasashen Afrika ba su tabbatar ko za su janye jiki daga cikin babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya ko a'a ba. Ban da wannan kuma, akwai wasu kasashen da suka nuna goyon baya ga kotun, kamar Botswana. Manazarta sun bayyana cewa, akwai sabanin da ke tsakanin kasashen Afrika game da kwata-kwata janye jiki daga cikin babbar kotun binciken manyan laifuffuka ta duniya, sabo da haka, akwai wuya ainun wajen cimma matsaya guda a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China