Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Talatan nan ta sanar da cewa, har yanzu tana rike da kashi 12 ne a cikin 100 na kasonta na rancen kudin da ta kan bayar, kamar yadda shugaban bankin tsakiyar kasar Sanusi Lamido Sanusi ya tabbatar wa manema labarai bayan taron kwamitin tsari na asusun ba da lamudi na duniya da aka yi a Abuja.
Malam Sanusi ya yi bayanin cewar, kwamitin tsari na asusun ya lura da cewa, matakin da aka dauka a taron shin a baya ya ba da kafa wajen aiwatar da kudurin taimakawa kudin cikin gida wato naira kaucewa shiga halin da kudaden wassu kasashen a nahiyar suka fada, inda hakan ya ba shi damar daidaituwa dan kadan.
Shugaban bankin ya ce, matakin lura da kudade da hukumar adana kudade ta Amurka ta dauka yana da kyau ga kudaden albarkatun mai na duniya.
Ya ce, dukkan mambobin kwamitin sun jefa kuri'ar amincewa na cigaba da ajiye kashi 50 a cikin 100 na kudin ajiya da ake bukata a fannin kudaden ayyukan al'umma, sannan kashi 12 a cikin 100 a bangaren ayyukan da ba na gwamnati ba, yana mai bayani ga manema labarai cewa, kwamitin har ila yau ya amince da cigaba mai karko da aka samu a bangaren tattalin arziki, musammam ma ta hanyar daidaita hauhawar farashin kayayyaki, daidaito a fannin kudi da kuma kudaden dake kasuwanni.
Malam Sanusi Lamido ya kara da cewa, fiye da kasashe 30 ne aka yi nazarin su, darajar kudin musanyar najeriya wato naira na daga cikin wadanda suka samu daidaito na lokaci mai tsawo, ganin ya rage daraja da kashi 2.3 a cikin 100 idan aka kwatanta shi da darajar sauran kudade na wassu kasashe da suka wargaje kasa sosai. (Fatimah)