Bankin duniya ya baiwa gwamnatin Mali taimakon kudi na dalar Amurka miliyan 50 a ranar Laraba domin kyautata tsarin ba da hidima ga kasa. An sanya hannu kan takardun yarjejeniyar wannan taimakon kudi tsakanin mataimakin shugaban bankin duniya reshen shiyyar Afrika da ministar kudi da tattalin arzikin kasar Mali, madam Bouare Fily Sissoko, wadda ta bayyana cewa, wannan taimako ya zo lokacin da ake bukatarsa, baya kuma ga yawan alkawuran da aka yi wa kasar Mali. Wadannan kudade na dalar Amurka miliyan 50, wata babbar dama ce ga kasar Mali kuma za'a yi amfani da su yadda ya kamata. A nasa bangare, mataimakin shugaban bankin duniya reshen shiyyar Afrika mista Makhtar Diop ya bayyana cewa, wannan taimakon kudin zai taimaka wajen karfafa bangarorin zuba jari wadanda suka kasance masu muhimmanci ga kasar Mali tare da kara cewa, taimako ne dake cikin tsarin mulki na gari. Kafin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, shugaban bankin duniya reshen Afrika, tare da faraministan Mali Oumar Tatam Ly sun samu ganawa tare da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita. (Maman Ada)