in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta tsai da shirin shekaru 10 na amfani da tsarin kudi na kasashen Turai
2013-08-29 10:34:30 cri

Gwamnatin kasar Ghana a ranar Laraban nan 28 ga wata ta fitar da wani shiri na shekaru 10 da zai yi amfanin da wani tsarin kudi na kasashen Turai a cikin harkokin hada-hadar hannun jarinta.

A bayanin da ministan kudin kasar Seth Emmanuel Terkpet ya yi ya ce, masu hannun jari na cikin gida yanzu suna rike da miliyan 16.5 na dalar Amurka a cikin wannan sabon tsari da gwamnati ta fitar kuma da wannan adadin, masu hannun jari da masu shirin sayen hannun jarin za su iya cinikin su a kananan kasuwannin hannu jari na kasar.

Ministan ya jaddada bukatar da ke akwai wato a farfado da kasuwannin hada-hadar kudin na cikin gida domin samun isassun jarin ma gwamnati da masu zaman kansu, yana mai nuni da cewa, gibin dake tsakanin wannan fanni da kasar ke fuskanta za'a iya cike shi ne idan aka yi amfani da ribar dake ciki na dogon tsarin na daukan nauyi kamar na hada-hada kudin na gida da na waje.

Ya ce, tsarin kudin na kasashen Turai da kuma tsarin na shekaru 7 na cikin gida da aka fitar, wata alama ne daga gwamnati game da kudirinta na ganin ta zurfafa tare da fadada hanyoyin da za'a bi a amfana daga wadannan matakan.

Mr. Terkper don haka ya bukaci shugabannin hukumomin masu kula da fanshion jama'a, kudin ajiya da na bukatun walwalar jama'a da su yi amfani da wannan dama da hukumomin hannun jari na kasar suka samar.

Gwamnatin kasar Ghana dai a ranar 7 ga watan da muke cikin nan ne ta fitar da wani tsarin amincewa da amfani da tsarin hada-hadar kudin kasashen Turai na shekaru 10 da adadin kudin dalar Amurka biliyan daya da zai kasance daga kashi 7.875 a cikin 100. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China