in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta ci gaba da amfani da kudade na kasa daban daban domin makoma mai haske
2013-09-24 10:28:14 cri

Sabon ministan kudi na Zimbabwe Patrick Chinamasa ya ce, kasar za ta cigaba da amfani da kudaden kasashe daban daban domin samun makoma mai haske da neman daidaito na tattalin arzikinta.

Zimbabwe dai a yanzu haka tana amfani da kudaden dalar Amurka da rand na kasar Afrika ta Kudu da kuma pula na kasar Botswana tare da sauran kudaden wassu kasashe cikin kasuwanni bayan faduwar darajar dalar Zimbabwe lokacin wani matsin tattalin arziki da ya fada wa kasar a shekara ta 2008 da ta 2009.

Mr. Chinamasa ya samu yabo a kan fitar da sabon tsarin amfani da kudaden kasashen waje a cikin hada-hadar kudin kasar ta Zimbabwe a 'dan lokacin da ya rike mukamin ministan kudi na wucin gadi a watannin farko na shekara ta 2009.

Duk da dai cewa, shugabannin jam'iyya mai mulki ta ZANU-PF, har da shi kan shi shugaba Robert Mugabe suna korafin yadda kasar ba ta da takammamen kudin kanta, masana suna ganin cewar, kasar ba za ta yi gangancin sake bullo da dalar Zimbabwe ba a yanzu, kudin da su kansu al'ummar kasar suka raina darajarsa.

Ministan ya ce, domin a kau da duk wani shakku a zukatan al'umma, shi ya sa ya dawo gida don ya cigaba da amfani da wannan sabuwar dabara wadda za ta kasance a kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China