Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya yi tir da allawadai a ranar Litinin kan tashe-tashen hankalin baya bayan nan a kasar Masar, har ma da rikicin da ya barke a birnin Alkahira, da hare-hare kan jami'an tsaro da gine-ginen sojoji a kasar. Ban Ki-moon ya yi allawadai da babbar murya kan wadannan tashe-tashen hankali da suka faru a kasar Masar, inda mutane fiye da hamsin suka mutu a cikin hatsaniyar, a cewar wata sanarwar kakakin Ban Ki-moon. Akalla mutane 51 suka mutu a yayin da kimanin 270 suka jikkata a cikin fito na fito a ranar Lahadi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan 'yan uwa musulmi a lokacin bikin cikon shekaru 40 na yakin da kasar ta yi da Isra'ila a ranar 6 ga watan Oktoba. Mista Ban ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa dangoginsu tare da fatan samun lafiya ga wadanda suka jikkata.
Mista Ban ya jaddada muhimmancin yin zanga-zanga cikin lumana, da girmama 'yancin yin taro da kaucewa tashe-tashen hankali, a cewar wannan sanarwa.
Sakatare janar na MDD ya bayyana muhimmancin damawa da kowa cikin harkokin siyasa, girmama 'yancin 'dan Adam cikin kasa mai 'yanci da walwala a matsayin ginshikin tabbatar da tsarin demakaradiyya a kasar Masar, kuma su kansu hukumomin kasar Masar ya kamata su sanya gaba a cikin duk wasu ayyukansu. (Maman Ada)