in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin babban sakataren MDD zai tashi zuwa kasar Masar
2013-08-20 15:01:05 cri

Ran 19 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya sanar da cewa, ya riga ya aike da mataimakinsa mai kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman zuwa kasar Masar don yin shawarwari da hukumomin kasar kan kokarin kawo sulhuntawa da zaman lafiyar a kasar.

Yayin taron manema labaran da aka kira a hedkwatar MDD da ke birnin New York, Ban Ki-moon ya bayyana cewa, gwamnati da kuma shugabannin siyasa na kasar Masar sun dauki hakkin kawo karshen rikice-rikicen da kasar take fama da su, ya kamata su dukufa wajen kawo karshen wannan rikici, ta yadda za'a farfado tsarin demokaradiyya a kasar cikin sauri.

Ban Ki-moon ya bayyana cewa, a shirye take MDD na goyon bayan kasar Masar wajen warware matsalolin da kasar ke fama da su, shi ya sa, ya riga ya aike da mataimakin babban sakataren MDD da ke kula da harkokin siyasa Jeffrey Feltman zuwa birnin Alkahira, don yin shawarwari tare da bangarori daban daban da abin ya shafa tun daga bakin ranar 20 ga wata, kuma muhimmin batun da za a tattauna shi ne, yadda MDD za ta iyar ba da taimako wajen ayyukan shimfida zaman lafiya da kuma inganta fahimtar juna tsakanin bangarorin daban daban na kasar Masar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China