Wata kotun kasar Masar ta yankewa wani mai goyon bayan kungiyar 'yan uwa musulmi ko Muslim Brotherhood a Turance, hukuncin daurin rai da rai, bayan da ta same shi da laifin aikata wasu manyan laifuka da suka sabawa doka.
Kotun ta zargi mutumin tare da wasu 'yan kungiyar da laifin kaiwa jami'an tsaro hari, da cinnawa wasu majami'u biyu wuta, tare da kona wasu motocin tsaro masu sulke na miliyoyin daloli. Bugu da kari kotun ta tabbatarwa wadanda ake zargin laifukan barnata gine-ginen hukuma, da sanya shingaye a tituna, da kuma tada husuma a birnin Suez, bayan da jami'an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zanga a ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata.
Wata kafar yanar gizo mallakar kasar ta Masar ta bayyana cewa, cikin wadanda ake zargin mutum guda ne aka yankewa wannan irin hukunci mai tsanani, yayin da ragowar mutane 48 za su fuskanci daurin shekaru 5 zuwa 15 a gidan kaso, baya ga wasu mutane 12 da kotun ta sallama. (Saminu)