A ranar Litinin 23 ga watan nan na Satumba ne wata kotun kasar Masar ta zartas da hukuncin haramta ayyukan kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi, ko Muslim Brotherhood a Turance, wadda a baya ke matsayin kungiya mai zaman kanta.
Kotun ta kuma soke rajistar kungiyar, da ma dukkanin rassanta.
Wata kafar watsa labarun kasar ta sanar da cewa, kotun ta kuma ba da umarnin kwace dukiyoyin da kungiyar ta mallaka, wadanda za a sanya karkashin kulawar wani kwamiti, kafin zartas da hukunci na karshe don gane da hakan.
Tuni dai jagororin kungiyar suka yi Allah wadai da wannan hukunci, suna masu shan alwashin kalubalantarsa a gaban kotu ta gaba.
Da yake bayyana rashin gamsuwarsa don gane da wannan hukunci, wani mai magana da yawun reshen siyasar kungiyar, ya ce, kungiyar ta 'yan uwa musulmi za ta ci gaba da wanzuwa, duk kuwa da waccan sanarwa da aka bayar ta rushe ta.
Sai dai yayin da magoya bayan kungiyar ta Muslim Brotherhood ke kokawa, su kuwa tsagin gungun magoya bayan Tamarud, masu rajin kawar da gwamnatin tsohon shugaba Mohammed nuna goyon bayansu suka yi ga wannan hukunci. (Saminu)