in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morsi zai gurfana a gaban kotun hukunta masu aikata manyan laifuffka ta Masar
2013-09-02 13:08:36 cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya bayar da rahoton cewa, masu gabatar da karar na kasar Masar, sun bukaci tsohon shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsi da aka hambarar da wasu mutane 14 da su gurfana a gaban kotun hukunta masu aikata manyan laifuffuka ta kasar bisa zargin kashe wani 'dan jarida yayin boren da aka yi sakamakon wata dokar shugaban kasa mai sarkakiyar nan da ya gabatar a shekarar da ta gabata.

Babban mai shigar da kara Hesham Barakat, ya zargi Morsi da tayar da bore da aikata kisan gilla a yankin Itihadyah kusa da fadar shugaban kasa a ranar 5 ga watan Disambar shekarar 2012, bayan da abokan hamayyarsa suka nuna rashin amincewarsu da karin ikon da ya baiwa kansa.

Kamfanin dillancin labarai na MENA ya kara da cewa, dukkan mutane 14 da ake zargi 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi ne, jam'iyyar da ke goyon bayan Morsi.

Morsi ya kasance shugaban kasar Masar na farko da aka zaba bisa tsarin demokiradiya a tarihi a tsakiyar shekarar 2012, amma sojoji suka kifar da gwamnatinsa a ranar 3 ga watan Yulin shekarar 2013, bayan da miliyoyin 'yan kasar Masar suka bazama kan tituna, suna zarginsa da baiwa kansa ikon da ya wuce kima da kuma tabargaza da tattalin arzikin kasar.

Sai dai jam'iyyar 'yan uwa musulmi da magoya bayansu sun kira wannan yunkuri na sojojin a matsayin juyin mulki, inda suka rika gudanar da bore tare da bukatar ganin an maido da Morsi bisa mukaminsa.

Wannan lamari ya haifar da mummunan arangama tsakanin magoya bayan 'yan uwa musulmi da sojoji a karshen watan Yuli, inda sojojin suka kashe tare da jikkata dubban magoya bayan Morsi, lamarin da kasashen duniya suka yi Allah wadai da shi.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Masar, ta ce, a ranar Jumma'a, wani sabon fada ya barke, inda a kalla mutane 6 suka mutu, kana wasu 190 suka jikkata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China