Kasar Zimbabwe ta sa kafa ta shure a ranar Lahadi da zancen dake nuna cewa, ta sanya hannu cikin sirri domin samarwa kasar Iran sinadarin uranium da kuma ba da umurnin cabke 'yan jaridan nan biyu na jaridar kasar Burtaniya 'The Times' da suka ba da wannan labarin karya da ya fara rura wutar fargaban gamayyar kasa da kasa.
Mataimakin ministan ma'adinan kasar Zimbabwe Gift Chimanikire, da 'yan jaridar biyu suka rawaito kalamansa, ya shedawa jaridar gwamnatin Zimbabwe 'The Sunday Mail' cewa, bayanan da wadannan 'yan jarida biyu suka baiwa kafofin watsa labaru na kasar Burtaniya wata niyya ce ta son kai ta bata sunan kasar Zimbabwe. 'Labari ne na karya kuma mai hadari, ba mu da abin da za mu hako, balantana mu je da shi zuwa kasashen waje.' in ji mista Chimanikire kafin ya kara cewa, har yanzu gwamnatin Zimbabwe ba ta fara ba da lasisin harkar ma'adinai ba a halin yanzu, amma kuma ana cigaba da tono mai'adinai na mahakar Zambeze dake arewacin kasar mai arzikin albarkatun karkashin kasa.
Kasar Zimbabwe kasa ce dai da Allah ya horewa arzikin karkashin kasa mai tarin yawa musamman ma karfen Platine, Chrome, zinari, lu'u lu'u da karfe, haka kuma da tarin uranium.
Kasar Amurka da kawayenta na Turai sun aza wa kasar Iran takunkumin a bangaren makamashi domin hana kasar gudanar da ayyukanta na tace sinadrin uranium, bisa fargar kada kasar Iran ta mallaki makaman nukiliya. (Maman Ada)