Mahukuntan kasar Amurka sun yi kira ga kasar Iran da ta ba da cikakken hadin kai, ga kokarin da ake yi na magance cece-kucen da shirin sarrafa makamashin nukiliyar ke ci gaba da haddasawa.
Har ila yau gwamnatin Amurkar ta bukaci Iran din da ta baiwa hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, dukkanin goyon bayan da za ta bukata.
Cikin wata sanarwar da ta fito daga ofishin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Amurka Jen Psaki, ta rawaito Psaki na cewa, Amurka a shirye take, ta yi aiki kafada-da-kafada da sabuwar gwamnatin shugaba Hassan Rouhani, domin cimma burin da aka sanya a gaba.
Shi ma a nasa tsokaci, kakakin fadar White House Jay Carney, cewa ya yi, kofar Amurka a bude take ga mahukuntan kasar ta Iran, muddin dai suna da burin amincewa da kudurorin da kasashen duniya ke da muradin a aiwatar, kan batun shirin nukiliyar kasar. Sai dai Carney ya tabbatar da cewa, kawo yanzu, ba a shirya wata ganawa tsakanin shuwagabannin kasashen Amurka da na Iran din ba, duk kuwa da cewa, shuwagabannin biyu za su halarci babban taron MDD da za a gudanar a cikin makon nan. (Saminu)