Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta kasar ta ce, mutanen sun mutu ne lokacin da ake basu jinya sakamakon raunukan da suka samu, sai dai ana ganin yawan wadanda suka mutu na iya karuwa saboda tashin hankalin da ake fuskanta har yanzu a unguwannin Majengo da Kisauni saboda matasa suna nuna adawarsu ga kashe wani Shaihin Malami Ibrahim Ismael da mutane 3 da wadansu masu dauke da makamai suka yi a ranar Alhamis 4 ga wata.
Kakakin rundunar 'yan sanda Zipporah Mboroki ta karyata zargin da ake yi na cewar, jam'ian tsaro ne suka aikata wannan danyen aiki da ya janyo babban arangama tsakani 'yan sanda da matasa a tsawon ranar Jumma'ar nan.
Kwamandan 'yan sanda na birnin Mombassa Joseph Kitur ya ce, an tsaurara tsaro a birnin da wuraren da ke kewayensa domin tabbatar da cewar, masu yawo shakatawa sun ji dadin zaman su. (Fatimah)