in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran kungiyar Al-Shabaab ya yi barazanar karin hare-hare a Kenya
2013-09-26 14:59:03 cri

Jagoran kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta Al-Shabaab a Somaliya Ahmed Abdi Godane, ya yi barazanar ci gaba da kaddamar da hare-hare a sassan kasar Kenya, muddin dai mahukuntan kasar suka ki janye dakarun sojinsu dake jibge yanzu haka a kudancin Somaliya.

Godane ya kuma jaddada cewa, harin da magoya bayansa suka kaddamar ranar Asabar din da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 72, ramuwar gayya ne na ci gaba da kasancewar sojojin Kenyan a Somaliya.

Mahukuntan Kenyan dai sun bayyana yiwuwar samun karin mutanen da suka rasu sakamakon wannan hari, musamman wadanda ake tsammanin ginin cibiyar kasuwancin ya rubza da su, yayin da ake musayar wuta tsakanin maharan da jami'an tsaro.

Wannan barazana ta shugaban Al-Shabaab din na zuwa ne kwana guda, bayan sanarwar da mahukuntan Kenyan suka bayar, na murkushe yunkurin maharan kungiyar, wadanda suka kai hari ga wata cibiyar cinikayya mai suna Westgate, dake Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya.

Tun dai cikin watan Octobar shekarar 2011 ne Kenya ta tura dubban dakarunta zuwa kudancin kasar Somaliya, biyowa bayan garkuwa da mayakan kungiyar ta Al-Shabaab suka yi da baki 'yan kasar waje a Kenya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China