Rahotanni daga birnin Nairobi na kasar Kenya na nuna cewa, an kubutar da yawancin wadanda aka yi garkuwa da su a wani babban shago, kamar yadda kakakin rundunar tsaro ta sojin kasar Cyrus Oguna ya tabbatar wa manema labaran kasar a jiya Lahadi.
Oguna ya shaida wa kafar talabijin din kasar KTN cewar, an kubutar da yawancin wadanda aka yi garkuwa da su, sa'an nan jami'an rundunar soji sun yi wa shagon kawanya, bayan da wassu mutane da suka rufe fuskokinsu suka shiga wani babban shago a birnin Nairobi a safiyar ranar Asabar, inda suka fara harbi ta ko'ina, abin da ya hallaka mutane 68, nan take kuma ya jikkata fiye da 175, a cewar gwamnati, wannan harin yana da matukar muni tun bayan wanda aka kai a kan ofishin jakadancin Amurka dake kasar a shekara ta 1998.
Ana iyakacin kokarin ganin an gaggauta wannan aikin ceton, in ji kakakin rundunar tsaron, inda ya ce, yanzu haka 4 daga cikin jami'an rundunar tsaron sun ji rauni a lokacin wannan aiki, don haka an kai su asibiti domin neman magani.
A bayanin da gwamnatin kasar ta yi, ya zuwa wannan lokacin, akwai akalla mahara 10 zuwa 15 a cikin shagon da suka yi garkuwa da mutane, hakan ya sa aikin ceton yake da hadari kwarai.
A cikin wannan hari, 'yan kasashen wajen da suka rasa rayukansu a shagon akwai 'yan asalin kasar Faransa 2, na Canada 2, na Ingila 3, da Basiniya 1, sannan da 'dan kasar Ghana daya, tuni dai kungiyar 'yan tawaye ta Al-shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukan nauyin kai harin, inda ta ce, ramuwar gayya ce saboda kasar ta Kenya ta shiga kudancin Somaliya domin farautar 'ya'yanta a watan Oktoban shekara ta 2011. (Fatimah)