Wata sanarwa da majalisar gamayyar jam'iyyun siyarar ta Afirka(CAPP) ta bayar bayan kammala ganawar shugabanninta na kwanaki biyu da aka yi a birnin Lusaka babban birnin kasar Zambia,ta bayyana cewa, kotun ICC bata daidaita matsaloli tsakanin kasashen na Afirka bisa adalci,tana mai cewa, kotun na warware matsalolin nahiyar ce bisa muradun iyayen gijinta.kamar yadda sakataren gamayyar jam'iyyun Nafie Ali Nafie ya bayyana cikin sanarwar.
Ya ce jam'iyyun siyasun Afirka sun damu matuka cewa, kotun ta ICC tana zabe wajen gudanar da ayyukanta,domin ta fi karkata ga shugabannin Afirka,inda ta ke rufe idon ta ga irin ta'asar da shugabannin yammacin duniya masu fada aji ke aikatawa.(Ibrahim)