Bayan da aka yi bayani game da halin dangantakar dake tsakanin gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan na kasar Sin, mataimakin babban sakataren kungiyar sa kaimi ga samun zaman lafiya da dinkuwar kasa ta Sin Hao Yifeng ya yi kira ga Sinawan dake kasashen waje da su yi kokari tare da yin hadin gwiwa don sa kaimi ga samun moriyar juna yayin da ake yin mu'amala a tsakanin kasa da kasa tare da samar da yanayi mai kyau na samun zaman lafiya da dinkuwar dukkan kasar Sin.
A gun shawarwarin, shugaban kungiyar sa kaimi ga samun zaman lafiya da dinkuwar dukkan kasar Sin dake zaune a gabashin nahiyar Afirka Han Jun ya bayyana cewa, kungiyoyin Sinawa dake kasashen gabashin Afirka kamar kasar Kenya suna tsayawa tsayin daka kan yaki da duk irin aikin kawo baraka ga kasar Sin, kana suna fatan kasar Sin za ta samu dinkulewa cikin lumana tun da wuri. (Zainab)