Bisa labarin da aka samu, an ce, dalilin da ya sa aka rage hasashen da aka yi shi ne, sabo da mambobin kasashen kungiyar CEMAC sun rage fitar da man fetur. Duk da haka, kwamitin kula da manufofin kudi da bankuna na kasashen da ke tsakiyar Afrika ya ci gaba da nuna kyakkyawan fata game da karuwar tattalin arzikin kungiyar, wadda aka yi hasashe cewa, daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2016, matsaikacin yawan karuwar tattalin arzikinta CEMAC zai kai kashi 6 cikin 100.
Mambobin kasashen kungiyar ta CEMAC sun kunshi Burundi, da Kongo(Brazzaville), da Gabon, da Kamaru, da Kongo(kinshasa), da Chad, Afrika ta tsakiya, da Angola da wasu sauran kasashe 3.Babbar manufar kungiyar ita ce, inganta hadin gwiwar tattalin arziki a tsakanin kasashe mambobin kungiyar.(Bako)