in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a rufe hukumomin gwamnatin Amurka a sakamakon dasa shinge da jam'iyyar Republica ta yi, in ji shugaba Obama
2013-10-02 16:43:08 cri

A yammacin ranar 1 ga wata, shugaban Amurka Barack Obama ya yi jawabi ta kafar talibijin domin yin Allah wadai da jam'iyyar Republica da ta dasa shinge kan gudanar da shirin yin kwaskwarima ga kiwon lafiya da Obama da 'yan jam'iyyar Demokuradiyya suka gabatar, hakan ya yi sanadiyyar rufewar hukumomin gwamnatin kasar.

Shugaba Obama ya ce, domin dasa shinge ga shirin yin kwaskwarima kan kiwon lafiya kawai, da gangan ne wasu membobin majalisar wakilai 'yan jam'iyyar Republica suka haddasa rufewar hukumomin gwamnatin kasar Amurka, wannan ne karo na farko cikin shekaru 17 da suka wuce. A hakika dai da ma bai kamata wannan ya faru ba. A sabili da haka, Obama ya yi Allah wadai da membobin majalisar wakilai 'yan jam'iyyar Republica da su ta da zaune tsaye inda suka ki yarda da a ba da tabbacin kiwon lafiya irin wanda yawancin Amurkawa ke iya biya kudinsa, abin da ya haddasa rufewar hukumomin gwamnatin kasar.

A cikin jawabinsa, Obama ya sake bayani kan shirin yin kwaskwarima a kan kiwon lafiya, inda ya ce, rufewar hukumomin gwamnatin a wannan karo ba ta da alaka da kasafin kudi, sabo da shiri ne. Kuma ya ce, kawo yanzu babu wata masaniya kan babbar illar da za a samu a sakamakon hakan.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China