Wata sanarwar da darektar ofishin kasafin kudi na fadar White House ta Amurka Sylvia Burwell ta bayar ta ce, babu wata alamar da ke nuna cewa, majalisar dokokin kasar za ta dauki mataki a kan lokaci domin shugaban kasa ya sanya hannu kan kudurin da za a ci gaba da muhawara a kansa kafin yau 1 ga watan Oktoba ba, don haka kamata ya yi hukumomin su fara shirya rufewa, idan har ba a kai ga cimma wata matsaya game da wani kuduri ba.
Ta ce, mun bukaci majalisar da ta dauki mataki cikin hanzari, don samar da wata madafa na dogon lokaci da za ta tabbatar da samar da isasshen lokacin gabatar da kasafin kudi a ragowar shekarar kudi da ake ciki, tare da dawo da ayyuka da shirye-shiryen gwamnati da wannan al'amari zai shafa.
A jawabinsa shugaba Obama na Amurka ya ce, rufe hukumomin na gwamnatin, hakika zai yi tasiri kan tattalin arzikin Amurkawa, kuma wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 17 da gwamnatin Amurka ta rufe hukumominta.(Fatimah)