Kakakin rundunar tsaro ta JTF da ke yankin Laftanar kanar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan ga 'yan jarida a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.
Ya shaida wa 'yan jarida cewa, a halin yanzu ana yi wa mutane 8 daga cikin 12 da aka kama tambayoyi a garin Fatakwal, yayin da sauran mutanen 4 ake amfani da su wajen kula da jirgin ruwan da ke tsibirin Bonny.
Bugu da kari Laftanar kanar Nwachukwu ya ce, rundunar tsaro ta JTF din ta kwace sunduki dauke da lita 50,000 na danyen mai da aka samu a wata tashar da ake dakon mai ba bisa ka'ida ba, wanda ke kusa da gonar shimkifa da ke Burma tsakanin magudanar ruwar Brass da Obiama a karamar hukumar ta Brass a jihar ta Bayelsa.
Kakakin na JTF ya ce dakarun sun kuma kwace tare da lalata kwale-kwale guda 61 da ke dauke da albarkatun mai da ake zaton an sato a wasu sassan kudancin karamar hukumar Warri da ke yankin Delta.(Ibrahim)