Kafin taron na SCO sai da shugaba Xi ya ziyarci kasar Kyrgyzstan, inda bangarorin biyu suka amince su kara inganta dangantakar da ke tsakaninsu zuwa wani matsayi.
A yayin da ya ke rangadi a kasashen ketare, shugaba Xi Jinping ya ziyarci kasashen Turkmenistan, Kazakhstan da kuma Uzbekistan kana ya halarci taron kolin kasashen kungiyar G20 da aka yi a birnin St.Petersburg na kasar Rasha. (Ibrahim Yaya)