Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Siteny Andriasoloniaiko ya fada a yayin taron manema labarai a ranar Talata cewa, a hukumance tawagar kasar ta kunshi mutane 26, ciki har da 'yan wasa 7, masu horas da su, shugabannin tawagar, jami'ai daga kwamitin wasannin Olympics na kasar Madagascar da 'yan jaridu guda 3.
'Yan wasa guda 3 ne kawai suka samu nasarar zuwa gasar ta Olympics daga kasar Madagascar, wato Soloniaina Josiane Patricia a bangaren daga kayan nauyi na Kilogram 72 na mata, Fetra Ratsimiziva a bangaren wasan kokawar Judo na Kilogram 81 na maza, da kuma Nathalia Rakotondramanana a bangaren daga kayan nauyi na mata.
Har ila yau, Madagascar tana da wadanda za su wakilce ta bisa gayyatar musamman da aka yi musu, ciki har da 2 a bangaren ninkaya, wanda Fils Rabetsara Alain Estellah da Ramanantsoa Tsilavina Mamitina za su wakilce ta da kuma wasu a bangaren guje-guje guda 2 wanda Ali Kame da Saholinirina Eliane za su fafata.
Wannan dai shi ne karo na 12 da kasar ta Madagascar ke halartar gasar wasannin Olympics. (Ibrahim)