Mr. Pierrot Rajaonarivelo ya fadi hakan ne, a wajen liyafar taya murnar cika shekaru 40 da kafa dangantakar diplomasiya tsakanin kasar Sin da kasa ta Madagascar, da aka gudanar a ofishin jakadancin Sin da ke Madagascar, kuma ya nuna godiyarsa ga taimakon da Sin ta bai wa kasar Madagascar a cikin shekaru 40 da suka gabata.
Jakadan Sin da ke kasar Madagascar Shen Yongxiang ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa dangantakar diplomasiya, ya zuwa yanzu, a cikin shekaru 40 da suka gabata, dangantakar kasashen biyu ta cigaba da bunkasa cikin hali mai karko, bugu da kari, kasashen biyu, na nuna fahimtar juna da kuma goyon baya a dukkan harkokin kasa da kasa da na shiyya shiyya, tare kuma da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa mai amfani a fannonin tattalin arzikin da cinikayya, ayyukan ba da ilimi, da kuma zaman lafiya da dai sauransu. A cikin shekaru 3 masu zuwa, kasar Sin za ta kara karfafa hadin gwiwa da kasar Madagascar a fannonin ayyukan ba da ilmi da ba da horo ga kwararru. (Maryam)