in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage zaben Madagascar saboda karancin lokaci shirye-shirye
2013-02-06 16:23:23 cri
Hukumar shirya zaben kasar Madagascar ta bayyana dage zagayen farko na babban zaben kasar daga ranar 8 ga watan Mayu zuwa ranar 24 ga watan Yuli a bana.

A cewar shugaban hukumar ta CENIT Atallah Beatrice, hakan na da nasaba da karancin lokacin shirya zaben yadda ya kamata. Bugu da kari Beartrice ya ce, za a iya gudanar da zagaye na biyu na babban zaben, tare da na 'yan majalisu ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa, idan har akwai bukatar hakan, maimakon ranar 3 ga watan Yuli, da a baya aka shirya gudanarwa.

A ranar 1 ga watan Ogustan bara ne dai hukumar ta CENIT ta sanar da tsohon lokacin zaben, tare da na shuwagabannin kananan hukumomi da aka shirya gabatarwa a ran 23 ga watan Oktoba mai zuwa. Kafin daga bisani shugaban shirin mika mulkin kasar Andry Rajoelina ya bayyana rashin amincewarsa da wannan wa'adi a ran 15 ga watan Janairun da ya gabata.

Rajoelina ya kuma bukaci da a gabatar da zaben 'yan majalisu kafin na shugaban kasa, zaben da ba ya cikin 'yan takara.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China