in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin da ya barke a sansanin soji na Madagascar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3
2012-07-23 11:08:04 cri
Babban hafsa-hafsoshin dakarun kasar Madagascar Andre Ndriarijaona ya bayyana a ranar 22 ga wata da dare cewa, dakarun dake dauke da makamai sun mamaye wani sansanin soji da ke kusa da babban filin jirgin sama Ivato da ke birnin Tananarive hedkwatar kasar, inda aka yi musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin da dakarun da ke dauke da makamai, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 3, kuma yanzu, sojojin gwamnatin sun riga sun mamaye wurin.

Ma'aikatan da ke filin jirgin sama sun fada wa manema labaru cewa, sakamakon la'akari da harkokin tsaro, ya sa an dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen sama a wannan filin jirgin sama, kuma ba a san yaushe ne za a mai da zirga-zirgar jirgin sama ba.

Dakarun da ke dauke da makamai sun ta da zaune tsaye ne domin hana yin shawarwari tsakanin tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana da shugaban wucin gadi na yanzu Andry Rajoelina da za a yi a kasar Seychelles a ranar 25 ga wata, kamar yadda kafofin yada labaru suka bayar a kwanan baya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China