Amurka a jiya Alhamis 12 ga wata ta ce, rokon da kasar Syria ta gabatar na shiga kungiyar haramta amfani da makamai masu guba yana da amfani, amma ba hakan yana da nufin ba za a tantance tare da lalata wadannan makamai ba ne.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Marie Harf ta fada a wani taron manema labarai cewa, ta lura da bayanai da suka nuna cewa, kasar Syria ta fara shiga kungiyar haramta amfani da makamai masu guba na MDD, kuma wannan kungiya ita ce ke da ikon gudanar da yarjejeniyar hatamta amfani da makamai masu guba bisa kundin tsarin majalissar wanda ya amince da hana kasashen da suke cikin kungiyar amfani da makamai masu guba, cigaba da samar da makaman, amfani da su, adana su, canja musu wuirn zama, ko cigaba da ajiye su haka kawai.
Madam Marie Harf ta ce, Amurka ta amince da cewa, tabbas tsarin dokar hana amfani da makamai masu guba yana da muhimmanci wanda Amurka na cikin kasashen da suka amince da shi, sai dai wannan amincewar ta gwamnatin Syria ba tana nufin ba za'a hada hannu da ita Amurkan ba tare da Rasha wajen bincike domin a tabbatar, daga nan kuma a lalata wadanda aka boye ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry tun da farko ya fara tattaunawa a jiya da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov a Geneva game da yadda za'a mika makaman Syria karkashin sa idon kasa da kasa.
Marie Harf ta yi bayanin cewa, Mr. Kerry yana bukatar takamammen amincewa ne cewar, Rashan da gaske take bukatar ganin an bi diddigin zakulo makaman, tantance su, kwato su tare da lalata su gaba daya. (Fatimah)