in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka
2013-09-27 10:40:31 cri

A ranar Alhamis 26 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry a cikin tattaunawar bayan fage da a kan yi lokacin babban taron MDD karo na 68 da ake gudanarwa yanzu haka a cibiyar majalissar dake birnin New York.

Ban da yabawa da cigaban da aka samu a tattaunawar batun kasar Sham da kasashen mambobin kwamitin sulhu na MDD, Mr. Wang ya ce, kasar Sin ta kuma yaba kwarai da dattakon da ake nunawa wajen tattauna batun da kasashen da hakan ya shafa suke nunawa.

Ya kuma nuna fatan ganin an samu cigaba wajen warware batun makamai masu guba na kasar Sham ta hanyar siyasa wanda zai kawo babban cigaba cikin kwanciyar hankali maimakon daukan matakan soji.

Sin, in ji ministan, ta yi alkawarin cigaba da ba da gudummuwarta na ganin an warware batun na Sham cikin ruwan sanyi, don haka za ta hada hannu da sauran kasashen da abin ya shafa, don ganin an cimma hakan

Manyan jami'an kasashen biyu har ila yau sun tattauna batun nukiliya na zirin Koriya da na kasar Iran da kuma yanayin da ake ciki a yankunan Asiya da Pasifik. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China