Mr. Hong wanda ya bayyana rashin jin dadinsa ga aukuwar wannan lamari a madadin kasar Sin, ya kuma kara da cewa, kasarsa na nanata matukar bukatar tsagaita wuta, tare da gudanar da shawarwarin da za su kawo karshen yakin basasar kasar ta Siriya da ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa.
Ya ce, wajibi ne dukkanin bangarorin da wannan lamari ya shafa su yi biyayya ga dokokin harkokin diplomasiyya na kasa da kasa, wadanda suka tanaji ba da kariya ga ofisoshi, da ma'aikatan diplomasiyya ciki hadda na kasar ta Sin.
Rahotanni sun bayyana cewa, makamin wanda ya fada kan wani sashen ginin ofishin da misalin karfe 11 na safiyar ranar Litinin, ya rusa sashen ginin, tare da tarwatsa gilasan dake wasu sassansa. Ko da yake dai babu wanda ya rasa ransa sakamakon wannan lamari, an ce, wani karamin ma'aikacin dake ofishin ya samu rauni.(Saminu)