in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(sabunta)Rasha ta ce, 'yan tawaye ne suka kai hari da makamai masu guba a Damascus
2013-09-19 10:42:46 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha da ke ziyara a kasar Syria, Sergei Ryabkov, ya fada a ranar Laraba yayin taron manema labarai a ofishin jakadancin kasar Rasha da ke Damascus cewa, kasar ta Rasha ta samu karin shaidu daga Syria, da ke nuna cewa, 'yan tawaye ne suka yi amfani da makamai masu guba a Damascus, babban birnin kasar Syria.

Ya ce, hakika ba mu ji dadi ba, domin sifetocin MDD ba su mayar da hankali sosai kan shaidun Syria ba, ganin cewa, a fili suke kuma suna da muhimmanci, don haka, kwararrun kasar Rasha za su yi nazari a kansu.

A ranar Talata ne wata tawagar kasar Rasha ta isa kasar Syria, domin ta tattauna da jami'an kasar game da yarjejeniyar baya-bayan da aka cimma tsakanin Rasha da Amurka da nufin daidaita batun zargin da ake yiwa kasar na kai hari da makamai masu guba.

Kasar Rasha ta gabatar da wani shiri na sanya makaman Syria masu guba karkashin sa-idon kasa da kasa, don hana yiwuwar Amurka na kai mata harin soja, bisa zargin da ake yiwa sojojin Syria na amfani da makamai masu guba kan fararen hula a wajen Damascus a ranar 21 ga watan Agusta.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mista Hong Lei, ya bayyana a ranar 18 cewa, kasar Sin tana mara wa kwamitin sulhu na MDD baya don ya taka muhimmiyar rawa kan batun da ya shafi zaman lafiya da tsaro. Haka kuma, a cewar Mista Hong, kasar Sin na fatan ganin an warware maganar makamai masu guba na kasar Sham ta hanyar siyasa, da gudanar da aikin lalata makaman karkashin tsarin MDD, yayin da ake kokarin daidaita batun ta hanyar shawarwari. Kasar Sin a nata bangaren na son mu'ammala da bangarorin da batun da ya shafa, in ji Mista Hong. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China