in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon MDD game da batun Syria
2013-09-26 20:37:31 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya fada a ranar Alhamis cewa, kasar Sin tana bukatar kwamitin sulhu na MDD da ya hanzarta cimma matsaya game da wani daftarin kuduri kan makamai masu guba na kasar Syria.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, kwamitin sulhun yana aikin bullo da wani daftarin kuduri gama de makamai masu guba na kasar Syria, amma ana samun rarrabuwar kawuna game da ko kamata ya yi kudurin ya kasance karkashin babi na 7 da dokokin MDD, wanda ya hada da yiwuwar amfani da matakin soja.

Hong Lei ya ce, har kullum kasar Sin tana shiga a dama da ita a tattaunawar da ake yi ta hanyoyin da suka kamata kuma a shirye take ta tattauna da bangarorin da abin ya shafa don ganin an hanzarta cimma matsaya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China