in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana iya kawo karshen rikicin Syria cikin 'yan makwanni, in ji ministan harkokin wajen kasar
2013-09-29 21:00:30 cri

Ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria Walid al-Moallem, ya bayyana cewa, abu ne mai sauki a kawo karshen rikicin kasar cikin 'yan makwanni, muddin kasashen dake baiwa 'yan tawayen kasar tallafi suka dakatar da yin hakan.

Moallem ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da wani gidan talabijin mallakar kasar Rasha. Ministan ya kara da cewa, da zarar irin wadannan kasashe masu goyon bayan 'yan tawayen kasar sun rungumi managarcin tsarin siyasa, za a kaiwa ga cimma nasarar kawo karshen yakin basasar kasar da ya ki-ci-ya ki-cinyewa.

Dama dai tuni Moallem ya bayyana wannan ra'ayi nasa gaban mahalarta babban taron MDD na bana, inda ya ce, dauki ba dadin da dakarun sojin gwamnatin kasar ke yi da 'yan tawaye ba zai kare ba, muddin Amurka da kasashen Turai, da ma wasu daga kasashen yankin Gulf suka ci gaba da taimakawa mutanen da ya kira 'yan ta'adda. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China