MDD ta fada a ranar Litinin cewa, an yi amfani da makamai masu guba da dama a garin Ghouta na kasar Syria a ranar 21 ga watan Agusta, lamarin da ya haddasa asarar rayukan jama'a, musamman tsakanin fararen hula da yara da dama.
A cikin wata wasika da shugaban tawagar masu binciken zargin yin amfani da makamai masu guban na MDD a wajen birnin Damuscus, babban birnin kasar Syria, Ake Sellstrom ya mikawa babban sakataren MDD tare da rahoton binciken, ya ce, akwai shaidun rokokin da ke nuna cewa, an yi amfani da sinadarin Sarin.
Sellstrom ya ce, bisa shaidun da suka samu yayin gudanar da bincike kan harin da aka kai a Ghouta ya nuna cewa, an yi amfani da makamai masu guba da dama. Jami'in ya ce, shaidun da suka tattara daga kasar wurin, samfurin sinadarai da sauran abubuwa, sun nuna karara cewa, rokokin da aka yi amfani da su a Ein Tarma, Moadamiyah, da Zamalka a yankin Ghouta dake Damascus suna dauke da sinadaran Sarin a jikinsu, sakamakon da shugaban tawagar ya ce, hakika ya sanya su cikin damuwa.
Aikin wannan tagawa dai shi ne ta binciko ko an yi amfani da makamai masu guba a Ghouta a yakin basarar da aka shafe sama da shekaru biyu ana gwabzawa a kasar, ba wai wanda ya yi amfani da makaman ba, inda aka yi zargin daruruwan mutane sun mutu sakamakon harin.
Sai dai dukkan bangarorin biyu, wato gwamnatin Syria da bangaren 'yan tawayen kasar, suna zargin juna da amfani da makamai masu guba a harin.
Yayin wata ganawar kwamitin sulhu na MDD a asirce, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ce, yanzu dai tawagar binciken makamai ta MDD ta tabbatar da cewa, an yi amfani da makamai masu guba a Syria, lamarin da Ban Ki-moon ya ce, hakan aikata laifuffukan yaki ne, kuma ya keta yarjejeniyar shekara ta 1925 da sauran dokokin kasa da kasa.
Mr. Ban ya ce, wannan al'amari ne da ya kamata a yi Allah-wadai da shi, kuma nauyi ne na kasashen duniya da su hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki, tare da tabbatar da cewa, ba za a sake amfani da makamai masu guba a wajen yaki ba. (Ibrahim)