in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan ganin MDD ta cimma wani kuduri kan makamai masu guba na Syria
2013-09-26 14:47:18 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira a ranar Labara ga kwamitin sulhu na MDD da ya yi kokarin cimma wata yarjejeniya da kuma amincewa da wani kuduri game da batun makamai masu guba na kasar Syria idan har dama ta samu. 'Bisa yin haka, mu isar da sakon hadin kai, da damar ba da taimakon siyasa ga yin bincike, tantancewa da kawar da makamai masu guba a kasar Syria.' in ji mista Wang a yayin wata liyafa tare da sakatare janar na MDD, mista Ban Ki-moon da kuma ministocin harkokin wajen kasashe hudu dake cikin kasashe biyar mambobin din din din na kwamitin tsaro.

Mista Wang ya jaddada cewa, hanyar siyasa ita ce hanya daya tilo wajen warware rikicin kasar Syria, ba wai daukar matakin soja ba.

Haka kuma ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da kara rubanya kokarinsu domin warware rikicin Syria ta hanyar shawarwari da kuma bayyana fatansa na ganin an kira taron Geneva na biyu kan batun Syria, inda za'a samu halartar bangarorin dake gaba da juna na Syria da muhimman kasashen da wannan rikici ya shafa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China