Har wa yau kuma, a wurare daban-daban na kasar Sin, an shirya bukukuwa da dama a kokarin nuna fatan alheri ga kasar. A birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudancin kasar Sin, dalibai kusan dari 2 daga makarantun firamare da sakandare sun daga tutar kasa, da rera taken kasar, a kokarinsu na nuna kishin kasa. A birnin Changchun na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar, mutanen dake rike da tutar kasa sun sanya tufafin gargajiya, da rera wakoki tare, domin murnar wannan rana.
A ranar 30 ga watan Satumba, a birnin Beijing, an shirya liyafar murnar biki na kasa, inda aka yi murnar cika shekaru 62 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Wasu manyan shugabannin kasar Sin, ciki har da Hu Jintao, da Wu Bangguo, da Wen Jiabao tare da mutane sama da dubu 1 daga bangarori daban-daban daga cikin gida da waje sun halarci liyafar cikin annashuwa.
Firaministan kasar Sin Mista Wen Jiabao ya gabatar da jawabi a yayin liyafar, inda ya ce, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 90 cif da kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma shekara ce da aka soma aiwatar da shirin raya kasa nan da shekaru biyar. Don haka kamata yayi a ci gaba da neman bunkasuwa bisa kimiyya, da kara samar da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'a, da ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. Ta hanyar yin kokari ba tare da kasala ba, za'a kafa wata kasa mai wadata dake bin tafarkin gurguzu.(Murtala)