in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijeriya ya kira liyafa domin murnar ranar cika shekaru 63 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2012-09-21 10:58:57 cri

A ran 20 ga wata, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijeriya ya shirya liyafa domin taya murnar ranar cika shekaru 63 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Karamin ministan harkokin waje na kasar Nijeriya Dr. Nurudeen Mohammed, wanda ya wakilci shugaba kasa Goodluck Jonathan, da jakadun kasa-da-kasa da ke Nijeriya, da kuma wakilai da suka zo daga hukumomin kasar Sin da ke Nijeriya sun halarci wannan liyafa.

Jakadan kasar Sin da ke Nijeriya Mista Deng Boqing, ya ce, ya shafe shekaru 2 yana aiki a Nijeriya, a cikin wadannan shekaru biyu ya fahimci muhimmiyar rawa da Nijeriya ke takawa a Afirka, kuma ya ga kyakykyawan sakamakon da kasashen Sin da Nijeriya suka samu, wajen hadin kansu da moriyar juna.

Dr. Nurudeen Mohammed ya ce, ya halarci wannan liyafa ne domin wakiltar shugaba Jonathan, amma shi da kansa wani abokin arziki ne ga kasar Sin, ya kara da cewa, kasar Sin ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa, dan haka Nijeriya za ta kara raya dangantakarta da kasar ta Sin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China