in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijar ya shirya liyafa don murnar zagayowar ranar kafuwar kasar Sin
2012-09-30 17:39:38 cri
A kwanan nan, jakadan kasar Sin da ke Jamhuriyar Nijar Shi Hu ya shirya liyafa a ofishinsa don taya murnar ranar cikon shekaru 63 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin. Shugaban kwamitin kula da tattalin arziki da zamantakuwar al'umma kana da al'adu na Nijar, shugaban kwamitin bayar da lambobin yabo na kasar, wakilin firaministan kasar, ministan makamashi da man fetur na kasar, mataimakin shugaba na farko na majalisar dokokin kasar, babban kwamanda na sojojin kasar, gwamnonin jihohin Niamey, Agadaz, da kuma Zinder, jakadun kasa da kasa da ke Nijar, wakilan kungiyoyin kasa da kasa, kana da wakilan Sinawa da ke zaune a kasar, bakin da yawansu ya kai kimanin 400 a baki daya sun halarci wannan liyafar.

A cikin jawabin da ya yi, jakada Shi Hu ya waiwayi manyan nasarorin da kasar Sin ta samu tun bayan kafuwarta, musamman ma kan saurin bunkasuwar tattalin arzikinta har na tsawon shekaru 34 bayan da kasar Sin ta bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, har ma jimillar kudin da ta samu a fannin tattalin arziki wadda ta karu da sau 20. A sa'i daya kuma, ya nuna cewa, kasar Sin wata kasa ce mai tasowa, akwai jan aiki muddin ana son kawar da talauci kwata kwata a kasar. Jama'ar kasar Sin za su tsaya tsayin daka kan bin hanyar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, kana da neman samun ci gaba cikin lumana, dalilin da ya sa haka shi ne saboda wannan hanya ta canja kaddarar kasar Sin, da kuma kawo alheri ga jama'ar kasar biliyan 1.3.

Yayin da yake magana kan dangantaka a tsakanin Sin da Afirka, jakada Shi Hu ya bayyana cewa, kasar Sin tana yin iyakacin kokarinta don tallafawa kasashen Afirka wajen kara karfinsu na raya kansu, inganta muhimman ayyukan more rayuwar jama'a, horar da kwararru a fannonin aikin kula da masana'antu da fasahohi, kana da kara yawan kudin da take zubawa Afirka, yayin da kasar Sin ke kokarin raya tattalin arzikinta yadda ya kamata.

Game da dangantaka a tsakanin Sin da Nijar, jakada Shi Hu ya ce, bangarorin biyu su kan mara wa juna baya a kan wasu muhimman batutuwan da ke jawo hankalinsu, hakan ya sa sun zama aminai da ke amincewa da juna. Yanzu dangantaka a tsakanin Sin da Nijar ta shiga wani sabon zamani na samun saurin ci gaba daga dukkan fannoni. Babu shakka za a kara samun sabbin nasarori a kokarin raya huldar dake tsakanin kasashen 2, kana jama'ar Nijar za su ci moriya sosai daga ayyukan hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China