Firaministan kasar Sin Mista Wen Jiabao ya gabatar da jawabi a yayin liyafar, inda ya ce, shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 90 cif da kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma shekara ce da aka soma aiwatar da shirin raya kasa nan da shekaru biyar. Don haka kamata yayi a ci gaba da neman bunkasuwa bisa kimiyya, da kara samar da tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'a, da ci gaba da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje. Ta hanyar yin kokari ba tare da kasala ba, za'a kafa wata kasa mai wadata dake bin tafarkin gurguzu.
Har wa yau kuma, a ranar 1 ga wata da safe, wadda ta kasance zagayowar ranar cika shekaru 62 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, Hu Jintao, Wu Bangguo, Wen Jiabao da sauran shugabannin kasar sun je filin Tian'anmen dake birnin Beijing, inda suka gabatar da kambun furanni a gaban ginin tunawa da jaruman kasar Sin.(Murtala)