Dubban mutane, ciki har da shguaba Faure Gnassingbe da sauran kusoshin kasar da jakadun kasashen waje da ke kasar da wakilan hukumomin majalisar dinkin duniya dake kasar da wakilan bangarori daban daban na kasar sun halarci bikin. Haka kuma, mawaka da 'yan raye-raye wadanda suka fito daga kasashen Kwadivwa da Burkina Faso da sauran kasashen yammacin Afirka sun halarci bikin bisa gayyatar da aka yi musu.
A ranar 26 ga wata da dare, shugaba Faure Gnassingbe na Togo ya bayar da wani jawabi ga jama'ar kasar, inda ya yi fatan ganin 'yan kasar Togo sun yi kawar da takkadamar da ake samu a tsakanin jam'iyyun siyasa daban daban, ta yadda za su yi kokarin taimakawa wajen zamanintar da kasar Togo domin baiwa 'yan kasar Togo ne damar yiin mulki da kansu. (Sanusi Chen)