in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar Uzbekistan
2013-09-09 09:59:23 cri

A ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Toshkent a cikin wata ziyarar aiki a kasar Uzbekistan.)

A yayin ziyarar, Shugaban Xi zai gana da takwaransa na kasar Uzabekistan Abduganiyevich Karimov, kuma zai gana da shugaban majalisar dattijan kasar Ilgizar Sabirov, domin yin musayar ra'ayi game da karfafa dangantakar bangarorin biyu da yalwata hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu. Bisa labarin da aka samu, an ce, shugabannin kasashen biyu za su rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi tare da ba da sanarwar hadin gwiwa, kuma ma'aikatun da abin ya shafa da masana'antu na kasashen biyu su ma za su daddale jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China