Hong Lei ya ce, kamata ya yi kasashe shida da batun nukiliya na Iran ya shafa da ita kanta kasar Iran su sake yin shawarwari cikin hanzari don samar da sharadi wajen warware batun a dukkan fannoni yadda ya kamata. Sin ta nuna goyon baya ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su kara yin mu'amala da fahimtar juna don taimakawa wajen yin shawarwari a tsakanin kasashen shida da kasar Iran.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya yi wani jawabi a gun babban taron MDD karo na 68 a ranar 24 ga wata, inda ya ce, kasarsa ba za ta kawo barazana ga duniya ba, kana a shirye take wajen yin shawarwari kan batun nukiliyar kasar a karkashin wasu sharudan musamman. (Zainab)