Cikin wasikar, ma'aikatar harkokin wajen Syria ta bayyana cewa, shugaban kungiyar "Victory Front" ya taba bayar da jawabin bautawa kungiyar Al-Qaeda, wannan ya tabbatar da cewa, akwai alaka tsakanin kungiyoyin biyu, dalilin da ya sa, Syria ta bukaci MDD ta hukunta kungiyar "Victory Front" bisa kudurorin lamba 1267 da 1989 na kwamitin sulhu na MDD. Ma'aikatar ta kuma yi gargadin cewa, idan gamayar kasa da kasa ba su mai da hankali kan kungiyar adawa ta kasar Syria ta "Victory Front" da kuma magoyon bayanta ba, to za a fuskanci sakamako mai tsanani.
Kuma bisa labarin da aka samu, ran 9 ga wata, shugaban reshen kungiyar Al-Qaeda da ke kasar Iraq Baghdadi ya bayyana cewa, kungiyar "Victory Front" ta riga ta hada kai tare da kungiyarsa, shugaban kungiyar Ciorani ya sanar da bauta wa shugaban kungiyar Al-Qaeda Ayman al-Zawahri ran 10 ga wata. Bugu da kari, bisa kudurin MDD, duk wadanda suka kulla hulda da kungiyar Al-Qaeda, ya kamata gamayyar kasa da kasa ta rike kudade da kadarorinsu, hana su tafiye-tafiye, da dakatar da ba su makamai. (Maryam)