in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Kazakhstan sun yi shawarwari a birnin Almaty
2013-09-09 09:51:06 cri

A ranar 8 ga wata, shugaban kasar Kazakhstan Nursultan Nazarbayev ya raka takwaransa na kasar Sin Xi Jinping da ke ziyarar aiki a kasar zuwa birni mafi girma na kasar kuma cibiyar tattalin arziki, da al'adu ta kasar wato Alma-Ata.

A yayin ziyarar, bisa tambayar da aka yi masa, Xi Jinping ya gabatar da halin da ake ciki wajen raya tattalin arziki a kasar Sin. Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace ga bin hanyar karfafa aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, don sa kaimi ga canja salon bunkasuwa, da kyautata tsarin raya tattalin arziki. Yana mai cewa, al'ummar kasar Sin na da imanin raya tattalin arzikin kasar yadda ya kamata.

A nasa bangare, Shugaban Nazarbayev ya bayyana cewa, kasashen duniya suna mai da hankali a kan kasar Sin da ta kama hanyar raya zamantakewar al'umma irin ta gurguzu. Tarihi zai ba da shaida bisa gaskiya. Idan kasar Sin ta samu ci gaba, Kazakhstan ma za ta samu moriya. Sabo da haka, Kazakhstan tana fatan samun moriya daga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin hanzari, kuma tana fatan daidaita manyan tsare-tsare na raya kasa tare da kasar Sin, don su samu ci gaba tare. Bangarorin biyu sun amince da cewa, ziyarar Shugaban Xi a kasar ta samu nasara sosai, inda shugabannin kasashen biyu suka tsara alkiblar raya dangantakar kasashen biyu, tare da daddale wasu yarjejeniyoyin siyasa da na hadin gwiwa a tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China