Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Abuja, yayin da ya ke jawabi ga masu ruwa da tsaki a wannan bangare. Ya bayyana cewa, cikin daga cikin majemu 36 da ke kasar, guda 6 ne kacal ke iya samar da kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa ketare, don haka ya ce, ya umarci hukumar raya kanana da matsakaitan masana'antun kasar, asusun horas da ma'aikatan masana'antu ta hannun shirin bunkasa harkokin ciniyayya ta kasa, da su tantance dukkan majemun da ke Najeriya kana su yi aiki da masu shi don sake samar musu da kayan aiki kana a farfado da wadanda za a iya.
Ministan ya kuma bayyana cewa, sun gano kananan wuraren jima a shiyyoyi 6 na kasar da ake saran daga darajarsu zuwa matsayin kasa da kasa cikin watanni 18, wadannan a cewar ministan sun hada da Kano, Kaduna, Aba da sauransu.
Majemar da ke birnin Kano ta kasance daya daga cikin mafiya muhimmanci a Yammacin Afirka kana tana samun fatu da kiraga daga wajen Najeriya domin biyan bukatunta.
Ya jaddada cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta himmatu wajen samar da yanayin harkokin kasuwancin da ya dace, ta hanyar rage kudin tafiyar da kasuwanci domin a bunkasa wannan bangare ta yadda zai iya gogayya a kasuwannin duniya. (Ibrahim)