0914murtala.m4a
|
Kwamishiniyar kiwon lafiya ta jihar Borno dake tarayyar Najeriya Dr. Salma Anas-Kolo, ta bayyana a jiya Jumma'a cewa, an samu sabbin mutane 14, wadanda suka kamu da cutar shan-inna ko Polio a turance a jihar, adadin da aka bayyana a matsayin mafi yawa a baya-bayan nan a dukkanin fadin kasar.
Dr. Salma ta ce, hare-haren da 'yan kungiyar nan ta Boko Haram suke kaiwa a sassa daban-daban na jihar sun kawo cikas ga ma'aikatan kiwon lafiya, wajen yiwa yara kanana allurar rigakafin cutar ta shan-inna.
Kwamishiniyar wadda ta bayyana hakan a fadar mai girma shehun Borno, Alhaji Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi, yayin wani shirin fadakar da kan sarakunan gargajiya, ta ce cikin wannan adadi, an samu yara shida a kwayar birnin Maiduguri, da kuma hudu a yankin karamar hukumar Jere.
Dr. Salma ta ce, sarakunan gargajiya su ne suka fi kusa da al'umma, don haka za su iya taka muhimmiyar rawa wajen warware wannan matsala.
Kwamishiniya ta ce, gwamnatin Najeriya tana matukar kokarin cimma burin kawar da cutar shan-inna baki daya, matakin da ya yi daidai da kudurin hukumar kiwon lafiya ta duniya na kawar da cutar shan-inna a dukkanin fadin duniya nan da shekara ta 2014.
A nasa bangare, shehun na Borno, kira ya yi da iyaye da su tabbatar an yi wa yaransu kanana har ya zuwa 'yan shekaru 5 allurar ta rigakafin cutar shan-inna, yana mai cewa, bai kamata mutane su ci gaba da yada jita-jitar cewa wai, ana yin allurar ne da nufin rage yawan haihuwa ba. (Murtala)